Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiAn Kuɓutar Da Uwa Da ’Ya’yanta 3 Bayan Biyan Kuɗin Fansa Naira...

An Kuɓutar Da Uwa Da ’Ya’yanta 3 Bayan Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 4 a Enugu

Wata mata mai suna Mrs Bridget Okey da ’ya’yanta maza uku sun samu ’yanci bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Enugu ta Najeriya.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, an yi garkuwa da matar da ’ya’yanta, Chukwubuike, Chukwuemeka da Chijioke, ne a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, yayin da suke girbin rogo a gonarsu da ke Ugbene Ajima, a ƙaramar hukumar Uzo-Uwani.

An sace su ne a yankin Nwiyi Ivuruge, a kan hanyar zuwa ƙauyen Umualogo da ke makwabtaka da al’ummar Nkpologu.

Wata majiya da ke kusa da iyalan ta bayyana cewa masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa har Naira miliyan 40, amma daga bisani suka amince da karɓar Naira miliyan 4.

Majiyar ta ce an samu kuɗin ne ta hanyar gudummawar ’yan uwa, abokan arziki da sauran al’ummar yankin domin ganin an kuɓutar da iyalan.

Sai dai shugaban ƙaramar hukumar Uzo-Uwani, Barista Chijioke Ezugwu, ya musanta cewa an biya kuɗin fansa, inda ya ce jami’an tsaro ne suka yi nasarar kuɓutar da mutanen ta hanyar haɗin gwiwar ayyukansu.

Ezugwu ya yaba da ƙwarewa da jajircewar jami’an tsaron, yana mai cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen wannan musiba.

Ya kuma tabbatar da cewa ƙaramar hukumar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro wajen ƙarfafa tattara bayanan sirri da sa ido domin hana sake aukuwar irin wannan hari.

Shugaban ya buƙaci al’ummar yankin da su kasance masu sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da suka gani na zargi ga jami’an tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments