HomeSashen HausaJirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa...

Jirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa Ta Zuwa Katsina

-

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin tsayar da wani jirgin sama na kamfanin Rano Air mai lamba 5N-BZY, biyo bayan wata matsala da aka ruwaito cewa injin jirgin ya tsaya cak yayin da yake kan hanyarsa daga Abuja zuwa Katsina.

Wannan shawarar ta biyo bayan tsauraran matakan da NCAA ke ɗauka don tabbatar da bin ƙa’idojin tsaron jiragen sama a duk kamfanonin jiragen sama da ke aiki a sararin samaniyar Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin tafiyar, an samu matsala a inji na farko na jirgin, wanda hakan ya sa aka ga hayaƙi a cikin jirgin. Nan take ma’aikatan jirgin suka kunna na’urar bada iskar oxygen tare da ɗaukar duk matakan gaggawa don shirya sauka lafiya. Majiyoyi sun bayyana cewa hayaƙin ya ɓace kafin sauka, kuma jirgin ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba.

A wani rahoto da Katsina Post ta fitar, sai dai lamarin ya haifar da cikas ga jadawalin zirga-zirgar jiragen na Rano Air, inda ya bar fasinjojin da za su tashi daga Sokoto a filin jirgi. An tura wani jirgin ceto domin ɗaukar fasinjojin Abuja-Katsina, amma an soke tafiyar ta Sokoto.

Rahoton farko daga NCAA ya nuna cewa, Sashen Kula da Ingancin Jiragen Sama ya bayar da umarnin tsayar da jirgin har sai an kammala cikakken bincike.

“Injiniyoyi suna binciken jirgin a halin yanzu don gano ainihin musabbabin matsalar injin da kuma hayaƙin,” in ji rahoton.

Hukumar ta NCAA ta sake jaddada cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba wajen bin ka’idojin jiragen sama, ko da kuwa hakan zai haifar da cikas ga ayyukan zirga-zirgar jiragen.

NCAA ta yi alkawarin fitar da Karin bayani kan lamarin da zarar an kammala bincike kan jirgin mai lamba 5N-BZY.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular