Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiJirgin Air Peace Ta Yi Gaggawar Sauke Fasinjanta Bayan Yin Wata Barazana

Jirgin Air Peace Ta Yi Gaggawar Sauke Fasinjanta Bayan Yin Wata Barazana

Ma’aikatan kamfanin jirgin sama na Air Peace sun sauke wani fasinja mai suna Celestine Ezeudu bayan ya yi cacar baki da ma’aikatan jirgin tare da furta kalaman da suka tayar da hankalin jami’an jirgin.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ce ta bayyana hakan, inda ta ce lamarin ya jawo jinkirin tashin jirgin bayan matuƙin jirgin ya bayar da umarnin mayar da shi wurin ajiye jirage.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na hukumar, Michael Achimugu, ya ce lamarin ya faru ne a jirgin Air Peace mai lamba P47866, wanda zai tashi zuwa Asaba da ke Jihar Delta.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a daren Litinin, fasinjan ya ƙi bin umarnin ma’aikatan jirgin na dakatar da ɗaukar hotuna tare da ajiye wayarsa yayin da ake shirin tashin jirgin.

A yayin cacar bakin ne Ezeudu ya furta cewa: “Fushin da nake ji zai iya ƙona wannan jirgin.”

Bayan jin kalaman nasa, ma’aikatan jirgin sun sanar da matuƙin jirgin nan take, wanda ya bayar da umarnin mayar da jirgin wurin ajiye jirage da misalin ƙarfe 3:57 na yamma domin sauke fasinjan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments