Wednesday, November 18, 2026
HomeLabaraiKotu Ta Tabbatar Da Tijjani Gandu a Matsayin Ɗantakarar NDC a Kano

Kotu Ta Tabbatar Da Tijjani Gandu a Matsayin Ɗantakarar NDC a Kano

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da Hon. Tijjani Husaini Gandu a matsayin sahihin ɗantakarar jam’iyyar NDC a zaɓen fidda gwani na mazaɓar Kano Municipal, bayan ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar zaɓensa.

Ƙarar, wadda Hon. Aminu Ishak Yusif ya shigar, ta nemi kotun ta soke nasarar Tijjani Gandu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, bisa dalilan da mai ƙarar ya gabatar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sai dai Mai Shari’a Simon Amobeda, wanda ya jagoranci zaman kotun, ya yi watsi da ƙarar bayan mai ƙarar ya kasa gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da cewa ya sayi fom ɗin neman takara ko kuma ya halarci zaɓen fidda gwanin da ake takaddama a kai.

Kotun ta bayyana cewa rashin gabatar da irin waɗannan hujjoji ya raunana ƙarar, lamarin da ya sa ba ta samu dalilin amincewa da buƙatar mai ƙarar ba.

Hukuncin ya kawo ƙarshen ƙalubalen shari’a da aka yi wa nasarar Tijjani Husaini Gandu, tare da tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC a mazaɓar Kano Municipal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments