An gano gawar wani jariri a unguwar Kofar Na’isa da ke birnin Kano, ƙasa da sa’o’i 24 bayan gano wasu jarirai tagwaye biyu a unguwar Dorayi.
Wani ɗan gwagwarmaya, Comrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an gano gawar jaririn da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau.
A cewarsa, wani yaro ne ya buɗe wata leda da aka ajiye a wurin, inda ya tarar da gawar jaririn a cikinta.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya ƙara tayar da hankalin al’ummar Kano, musamman bisa yawaitar rahotannin gano jarirai da aka yi watsi da su a sassa daban-daban na birnin.
Hakan ya sake janyo kira ga hukumomin tsaro da na jin daɗin jama’a da su gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan dakile irin waɗannan al’amura.
