Jam’iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus ko kuma Majalisar Dokoki ta Kasa ta tsige shi, bisa zargin katsalandan a hukuncin Kotun Koli kan zaben gwamnan Kano na 2023.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce kalaman Gwamna Abba Kabir Yusuf a wata hira da BBC Hausa suka tayar da zargin cewa Tinubu ya yi amfani da Kotun Koli wajen cimma muradun siyasa.
ADC ta yi zargin cewa an samu wata yarjejeniya tsakanin Tinubu da Abba Yusuf, inda aka yi amfani da hukuncin kotu wajen musayar goyon bayan sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta ce idan aka tabbatar da zargin, hakan na iya zama babban laifi da ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Ta kuma bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa ta fara shirin tsige shugaban kasar tare da tilasta wa duk wadanda ake zargin suna da hannu a yarjejeniyar su gabatar da hujjojinsu.
Wannan na zuwa ne bayan Abba Yusuf ya bayyana a wata hira da BBC Hausa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanya shi ya yi rantsuwa cewa zai koma APC idan Tinubu bai yi katsalandan a shari’ar zaben gwamnan Kano ta 2023 ba.
A watan Janairun 2024 ne Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Yusuf, inda ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara da suka yi watsi da zabensa.
Yusuf ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC a watan Janairun 2026, lamarin da ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da Kwankwaso, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasararsa a zaben 2023.
