Thursday, November 26, 2026
HomeLabaraiTinubu Ya Taya Atiku Murnar Cika Shekaru 80 a Duniya

Tinubu Ya Taya Atiku Murnar Cika Shekaru 80 a Duniya

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa, tare da tuna yadda ya mara masa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2007.

Tinubu, a cikin saƙon taya murnar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ranar Laraba, ya yaba da gudunmawar Atiku ga ci gaban Najeriya, musamman a siyasa, ilimi da harkokin kasuwanci.

Ya ce ya goyi bayan takarar Atiku a zaɓen 2007 ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress a lokacin, saboda imanin cewa dimokuraɗiyya na bunƙasa ne idan aka bai wa ’yan siyasa damar gabatar da ra’ayoyi mabambanta.

Shugaban ya kuma yaba da kafa Jami’ar American University of Nigeria da Atiku ya yi a Yola, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen bunƙasa ilimi da samar da ƙwararrun ma’aikata.

Tinubu ya ce duk da cewa yanzu shi da Atiku suna jam’iyyu daban-daban kuma suna da saɓanin ra’ayoyi kan wasu batutuwa, haɗin kansu da kuma zaman lafiyar Najeriya ya kamata su kasance a gaba.

Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa tsakanin 1999 zuwa 2007, a halin yanzu shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.

Tinubu ya yi masa fatan ƙoshin lafiya da ƙarin shekarun hidima ga ƙasa da bil’adama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments