Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da mutuwar fursunoni uku yayin wani yunkurin tserewa daga gidan yarin Oke-Kura da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Babban Kwanturolan hukumar, Sylvester Nwakuche, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai Ilorin ranar Laraba.
Ya ce fursunoni bakwai ne suka yi yunkurin tserewa daga gidan yarin a ranar 18 ga Nuwamba, amma jami’an tsaro sun dakile biyar daga cikinsu, yayin da biyu suka samu nasarar tserewa.
Sai dai ya bayyana cewa fursunoni uku daga cikin waɗanda aka dakile sun mutu yayin faruwar lamarin.
Nwakuche ya ƙara da cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin mutuwar fursunonin, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci bisa doka.
Ya kuma bayyana cewa gidan yarin Oke-Kura tsohon gini ne da aka gina tun zamanin mulkin mallaka, wanda a yanzu ke fama da matsalar cunkoso.
A wani ɓangare na jawabin nasa, Nwakuche ya ce akwai fursunoni sama da 4,000 da aka yanke wa hukuncin kisa a gidajen yarin Najeriya.
Ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su sauya hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai, idan ba su da niyyar sanya hannu kan takardun aiwatar da hukuncin kisa.
