Saturday, November 28, 2026
HomeLabaraiTinubu Ya Yi Alkawarin Baiwa Manoma Lamunin Kuɗi Ba Tare da Ruwa...

Tinubu Ya Yi Alkawarin Baiwa Manoma Lamunin Kuɗi Ba Tare da Ruwa Ba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin samar wa manoma rancen kuɗi ba tare da ruwa ba, domin rage musu nauyin kuɗaɗen gudanar da noma, ƙara yawan amfanin gona da kuma sauƙaƙa farashin abinci ga ’yan Najeriya.

Tinubu ya bayyana haka ne a wajen gangamin zaɓen APC a Jihar Enugu, inda ya kuma yi alkawarin inganta samar da wutar lantarki, bunƙasa ababen more rayuwa da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin samar da yanayin da zai taimaka wa manoma su samu kuɗin gudanar da noma cikin sauƙi, domin ƙara samar da abinci da rage tsadar rayuwa.

Ya kuma buƙaci al’ummar Enugu da su fito su zaɓi APC a dukkan matakan zaɓe na gaba, yana mai cewa goyon bayan jam’iyyar zai taimaka wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments