Friday, November 27, 2026
HomeLabaraiAn Rantsar da Adeleke a Matsayin Gwamnan Jihar Osun Karo na Biyu

An Rantsar da Adeleke a Matsayin Gwamnan Jihar Osun Karo na Biyu

An Rantsar da Adeleke a Matsayin Gwamnan Jihar Osun Karo na Biyu

Gwamnan Jihar Osun da ke Najeriya, Sanata Ademola Adeleke, ya sake kama rantsuwar mulki a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar.

An rantsar da Adeleke ne a ranar Juma’a a filin wasa na Osogbo City Stadium, tare da mataimakinsa, Prince Kola Adewusi.

Alkalin Alkalai na jihar, Mai Shari’a Adepele Ojo, ce ta jagoranci bikin rantsar da su, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya a madadin Shugaba Bola Tinubu.

A jawabinsa bayan rantsuwar, Adeleke ya bayyana sake zaɓensa a matsayin nasarar muradin al’umma da kuma abin koyi wajen tabbatar da dimokuraɗiyya.

Gwamnan ya bayyana cewa ajandarsa ta wa’adin mulki na biyu za ta mayar da hankali kan walwalar jama’a, bunƙasa ababen more rayuwa, masana’antu, noma, tattalin arzikin zamani, yawon buɗe ido da bunƙasa matasa da mata.

Ya ce yana da burin sauya tattalin arzikin Osun daga wanda ya dogara da aikin gwamnati zuwa tattalin arzikin masana’antu.

Adeleke ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya shiga tsakani kan rikicin rabon kuɗaɗen ƙananan hukumomi, yana mai fatan za a warware matsalar gaba ɗaya cikin mako guda.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments