Gwamnan Jihar Plateau, Barrista Caleb Manasseh Mutfwang, a ranar Talata ya kaddamar da jami’an tsaro 1,450 da aka kammala horaswa a karkashin shirin Operation Rainbow, inda ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Da yake jawabi a filin wasa na Zaria Road Stadium, Jos, Gwamna Mutfwang ya bayyana tsaro a matsayin tushen da ake gina cigaba mai dorewa, tare da taya sabbin jami’an murnar kammala horaswarsu da kuma kudurinsu na yiwa al’umma hidima, Ya ce, Ba ku fi doka karfi ba a maimakon haka ku ne masu kareta da abokan aikinta.
Gwamnan ya bayyana cewa Operation Rainbow tsari ne na tsaro na al’umma da ke aiki kafada da kafada da Sojojin Najeriya, Yan Sanda, da Hukumar NSCDC, yana mai jaddada cewa dukkan ayyukan da jami’an keyi na karkashin kulawar kai tsaye, Ya kara da cewa rundunar na kare dukkan yan kasa ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ba.
Gwamna Mutfwang ya nuna cewa an dauko jami’an ne daga dukkan kananan hukumomi 17 na jihar, inda suka hada da Kiristoci da Musulmi. Ya tabbatar wa al’umma cewa manufar rundunar ita ce yakar aikata laifuka, ba nuna wariya ko kai hari ga wata kungiya ba. Ya kuma yi alkawarin cewa duk wata korafi da aka shigar kan jami’an za a bincika cikin gaggawa, tare da daukar matakin ladabtarwa idan an samu laifi.
Gwamnan ya kuma yaba da goyon bayan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, wajen yaki da barazanar tsaro a kasa baki daya. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta hada kai da Rundunar Sojin Najeriya domin amfani da na’urorin leken asiri ta sama (aerial surveillance) don karfafa tsaro, musamman a yankunan karkara a lokacin bukukuwan karshen shekara.
A karshe, Gwamna Mutfwang ya yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu sa ido da bin doka da oda, yana mai jaddada cewa tsaro nauyin kowa da kowa ne, tare da bukatar al’umma su mara wa Operation Rainbow baya ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ake zargin barazana ga tsaro.
