HomeSashen Hausa‎Jirgin Marar Matuƙi Ya Faɗo a Dajin Kontagora, Jihar Neja

‎Jirgin Marar Matuƙi Ya Faɗo a Dajin Kontagora, Jihar Neja

-

Wani jirgin marar matuƙi (drone) ya faɗo a wani daji da ke kusa da garin Kontagora, a Jihar Neja, da yammacin yau Juma’a, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ba tare da jikkata kowa ba, yayin da har yanzu ba a tabbatar da dalilin faɗuwar jirgin ba, Wasu mazauna yankin sun ce sun ji ƙara mai ƙarfi kafin daga bisani suka ga jirgin ya faɗo a cikin dajin.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro basu fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da mallakar jirgin ko manufar tashi da aka yi da shi.

‎Sai dai ana sa ran jami’an tsaro za su fara bincike domin gano musabbabin faɗuwar jirgin da kuma ko akwai wata barazana ga tsaron al’umma.

Hukumomi sun shawarci al’umma da su nisanci yankin da lamarin yafaru, tare da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali.

Za mu cigaba da bibiyar lamarin tare da kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na...

Manufar Kwankwaso Ita Ce Haddasa Rikicin Siyasa Da Bautar da Jama’ar Jihar Kano Kan Siyasa- Kano Youth Democratic Agenda

Kungiyar matasan da ke fafutikar dorewar mulkin dimokraɗiyya da shugabanci nagari a jihar Kano ta yi Allah wadai da manufar Kwankwaso wajen son haddasa rikicin...

Most Popular