HomeSashen HausaGwamnatin Gombe Ta Bai Wa Iyalan ’Yanjarida 7 Da Suka Rasu Tallafin...

Gwamnatin Gombe Ta Bai Wa Iyalan ’Yanjarida 7 Da Suka Rasu Tallafin Miliyan 14

-

Gwamnatin Jihar Gombe ta raba naira miliyan 14 ga iyalan ’yan jarida bakwai da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kan hanyar Billiri zuwa Kumo.

 

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya mika naira miliyan biyu ga kowanne iyali a matsayin tallafin kuɗi domin taimakawa wajen jana’iza da sauran buƙatu.

 

Njodi ya ce tallafin na daga cikin ƙudurin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na rage raɗaɗin rashi ga iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta ɗauki alhakin biyan kuɗaɗen jinya na ’yan jaridar da suka jikkata.

 

Ya kuma bayyana alhini kan asarar da ta rutsa da jihar da kuma harkar aikin jarida, yana mai jaddada cewa kuɗin ba diyya ba ne.

 

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Alhassan Yahaya Abdullahi, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta aiwatar da inshorar rayuwa da lafiya ga ’yan jarida.

 

Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Lauya Abubakar Ahmed ya yaba wa gwamnan, yana mai cewa tallafin zai taimaka matuƙa wajen biyan buƙatun gaggawa da na dogon lokaci na iyalan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

An Zaɓi Hon. Dauda Kurfi A Matsayin Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Kansiloli A Jihar Katsina

Tsofaffin Kansiloli, sun rushe shugabancin ƙungiyar tsofaffin Kansilolin ta ƙasa reshen jihar Katsina, inda suka zaɓi Hon. Dauda Kurfi, a matsayin shugaban ƙungiyar tsofaffin Kansiloli...

Dikko Radda Ya Amince Da Naɗin Sabbin Manyan Sakatarori a Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da naɗin sabbin manyan sakatarorin jihar.   Gwamnan ya ce an gudanar da naɗin bi sa cancanta da...

Most Popular