Akalla sojojin Najeriya tara ne suka mutu bayan da motarsu ta taka nakiyar bam a yayin wani aikin sintiri a wani yanki na jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce fashewar bam ɗin, wanda ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa, ta faru ne a lokacin da ayarin motocin sojoji ke wucewa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin nan take.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce an fara bincike kan lamarin tare da ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana sake aukuwar irin wannan hari.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a wasu sassan jihar Borno.
