HomeSashen HausaYawancin Fulanin Da Suke Ta’addanci Ba Su Da Addini, Ba Su San...

Yawancin Fulanin Da Suke Ta’addanci Ba Su Da Addini, Ba Su San Allah Ba– Nasir El Rufa’i ‎

-

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa yawancin mutanen Fulani da ake zargi da aikata ta’addanci da kashe kashe a sassa daban daban na ƙasar nan ba su da wata alaka ta gaskiya da addini, yana mai cewa ‘ba su san Allah ba’

‎El-Rufa’i ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da aka yada a kafafen sada zumunta, inda ya jaddada cewa bai dace a ɗora laifin ayyukan ta’addanci da tashin hankali kan wata kabila ko addini ba.

‎A cewarsa, mutanen da ke aikata kisan gilla, garkuwa da mutane da kuma tayar da zaune tsaye, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, suna amfani ne da sunan kabila ko addini domin boye muguwar manufarsu.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa akwai bukatar al’umma su daina kallon matsalar tsaro ta fuskar kabila ko addini, domin hakan na kara rarraba jama’a da kuma hana samun mafita ta gaskiya.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su kara mayar da hankali wajen gano hakikanin masu aikata laifuka tare da daukar tsauraran matakai a kansu, ba tare da nuna wariya ba.

Maganganun El-Rufa’i sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya, inda wasu ke ganin ya fadi gaskiya, yayin da wasu kuma ke cewa kalamansa na iya tayar da sabuwar muhawara kan rikicin kabilanci da na addini a kasar.

Duk da haka, masana harkokin tsaro na ganin cewa matsalar ta’addanci da ’yan bindiga a Najeriya na da sarkakiya, kuma tana bukatar hadin kai daga gwamnati, shugabannin addini, na gargajiya da kuma al’umma baki daya domin kawo karshen matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Received 29 New ASPs From The Nigeria Police Academy, Wudil

The Katsina State Police Command has received 29 newly posted Assistant Superintendents of Police (ASPs) from the Nigeria Police Academy, Wudil. Welcoming the officers, the...

DA DUMI-DUMI: Trump Ya Sake Yin Barazana Kan Ɗaukar Matakin Hari Ga ‘Yan Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara jefa sabuwar barazana ga Gwamnatin Najeriya, yana cewa zai ɗauki matakai masu tsauri ciki har da yuwuwar amfani da...

Most Popular