HomeSashen Hausa‎’Yan Garin Dutsinma Sun Nuna Farin Ciki Bayan Zaman Sulhu da Barayin...

‎’Yan Garin Dutsinma Sun Nuna Farin Ciki Bayan Zaman Sulhu da Barayin Daji

-

Al’ummar garin Dutsinma dake Jihar Katsina sun bayyana matuƙar farin ciki da jin daɗi biyo bayan zaman sulhun da aka kulla tsakanin jama’ar garuruwan dake fama matsala tsaro da barayin daji, wanda ya kawo sauƙi da natsuwa ga rayuwar mazauna yankin.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, sun bayyana haka ranar Laraba 14 ga watan Janairu 2026, lokacin da suke ganawa da Manema Labarai a kasuwar.

‎Da yake zantawa da wakilanmu, Malam Isah Dutsinma ya bayyana cewa kafin a cimma wannan sulhu, wasu sassan garin ba su da tabbacin tsaro, lamarin da ke sanya jama’a fargaba wajen zirga-zirga da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
‎“Yanzu mun samu kwanciyar hankali, muna iya yawo ba tare da fargaba ba,” in ji shi.

‎Ita ma Malama Bara’atu Muhammad, wata mazauniyar garin Dutsinma, ta bayyana jin daɗinta kan yadda dawowar zaman lafiya ya ba su damar ci gaba da rayuwa cikin walwala. Tare da bayyana cewa sulhun ya ƙarfafa zumunci da mu’amala a tsakanin jama’a, inda kowa ke iya ziyartar juna ba tare da wata matsala ba.

‎Wani magidanci a garin ya ƙara da cewa zaman sulhun ya zo da alkhairi mai yawa ga al’ummar Dutsinma, musamman wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya. A cewarsa, hakan zai taimaka matuƙa wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziƙi.

‎Al’ummar garin Dutsinma dai, sun bayyana fatan cewa wannan zaman lafiya zai dore, tare da kira ga dukkan ɓangarori da su kiyaye yarjejeniyar da aka cimma, domin tabbatar da ci gaba da rayuwa cikin tsaro da kwanciyar hankali a garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular