Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, Mataimakin Darakta, bisa zargin aikata badakalar kuɗi da ta kai Naira biliyan ɗaya.
Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bayan da waɗanda ake tuhumar suka musanta laifuka guda shida da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta tuhume su da aikatawa.
A cewar ICPC, ana zargin jami’an da karɓar kuɗaɗe har Naira miliyan 450, Naira miliyan 310 da kuma Naira miliyan 260 ba bisa ƙa’ida ba, a tsakanin watan Nuwamba da Disamba na shekarar 2024, kuɗaɗen da aka ce sun sabawa doka.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu, domin duba buƙatar belin waɗanda ake tuhuma, yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin da ake musu.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, lamarin dai ya ja hankalin jama’a, musamman ganin muhimmancin hukumar KANSIEC a tsarin dimokuraɗiyya da gudanar da sahihin zaɓe a Jihar Kano.
