Kungiyar Kwankwasiyya ta Najeriya ta sanar da nada sabbin masu magana da yawun ta guda biyu a matsayin wani mataki na karfafa saƙonnin siyasa da kuma kyautata hulɗa da al’ummar Najeriya.
An nada Hon. Habib Saleh Mailemo a matsayin Mai Magana da Yawun Kwankwasiyya na I, wanda zai kasance babban murya na kungiyar kan batun siyasa, manufofi, da shugabanci. Capt. Mansur Umar Kurugu kuma zai kasance Mai Magana da Yawun ƙungiyar na II, mai kula da daidaita saƙonni, bayar da amsa cikin sauri, da sadarwa zuwa matakin ƙasa.
Wadannan nadin, karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an tsara su ne domin ƙarfafa fahimta, daidaito, da ƙwarewa a cikin saƙonnin kungiyar a yayin da yanayin siyasa ke canzawa.
Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata, wanda ya wakilci kungiyar, ya ce dukkanin saƙonnin hukuma za a rika isar da su ta hannun sabbin masu magana da yawun, inda ya jaddada ci gaba da jajircewar Kwankwasiyya kan adalci, daidaito, da shugabanci mai inganci.
