Femi Falana, babban lauya mai kare haƙƙin ɗan ada, ya ce rundunar sojin Najeriya ta ruɗi jama’a ta hanyar musanta zargin yunƙurin juyin mulki a baya, yana mai cewa ya dace su ba ’yan Najeriya haƙuri.
Falana ya bayyana hakan ne bayan da hedikwatar tsaro ta tabbatar cewa akwai shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da sanar da cewa za a gurfanar da wasu jami’an soji a gaban kwamitocin shari’a na soji.
A watan Oktoban 2025 ne gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin ranar ’yancin kai, lamarin da daga baya aka danganta da zargin yunƙurin juyin mulki, duk da cewa hedikwatar tsaro ta musanta hakan a wancan lokaci.
Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels Television, Falana ya ce sabon bayani daga sojoji na nuna cewa an yaudari ’yan Najeriya, don haka ya zama wajibi a nemi afuwa.
Ya kuma ce bai dace a gurfanar da jami’an da aka tsare a kotun soja ba, domin zargin ya kai matsayin cin amanar ƙasa, wanda kotun tarayya ko ta jiha kaɗai ke da hurumin sauraro.
Falana ya ƙara da cewa jami’an da aka tsare suna da haƙƙin samun lauyoyi da ’yan uwansu, yana mai kira ga hukumomi su saki duk waɗanda ba a gurfanar da su a hukumance ba.
