Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba jimawa ba za ta kawo karshen rikicin da ya daɗe yana faruwa kan masarautar Kano, inda mutum biyu ke ikirarin kasancewa halastattun sarakuna.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce gwamnati ta tsara abubuwa na musamman domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan sarautar.
Kusan shekaru biyu kenan Kano na fama da rikicin sarauta, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a fadar Gidan Rumfa, yayin da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a fadar Nassarawa ƙarƙashin tsaron jami’an gwamnatin tarayya.
