Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano sun kama wani muhimmin mutum da ake zargi da badakalar mallakar Dala Inland Dry Port—wani shiri na biliyoyin nairori—a daidai lokacin da yake shirin barin jihar Kano ta jirgin sama.
An kama Ahmad Rabiu, tsohon Darakta Janar (Managing Director) na tashar jiragen ruwa ta tsandauri (Dry Port), kuma tsohon Kwamishinan Kasuwanci a Jihar Kano, ne a ranar Laraba a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, kamar yadda majiyoyi daga rundunar ’yan sanda suka tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa kama Rabiu na da alaka da zargin damfara da rikicin mallaka da ke tattare da Dala Inland Dry Port—lamarin da ya jawo cece-kuce a fagen siyasa da kasuwanci, inda ake alakanta shi da wasu manyan jiga-jigan gwamnati a baya, ciki har da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan tuhume-tuhumen da ake yi wa Rabiu ba. Sai dai majiyoyi sun ce ana ci gaba da bincike, kuma ana sa ran za a gurfanar da shi gaban kotu idan binciken ya kammala.
