Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMa’aikatan Lafiya a Katsina Sun Dakatar da Yajin Aikinsu Na Gargaɗi

Ma’aikatan Lafiya a Katsina Sun Dakatar da Yajin Aikinsu Na Gargaɗi

Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Jihar Katsina ta dakatar da yajin aikin gargaɗin kwanaki bakwai da ta fara gudanarwa, bayan samun tabbacin Gwamnatin Jihar na sake duba buƙatunta da nufin warware matsalolin da suka haddasa ɗaukar matakin.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Comrade Ibrahim A. Balange, ya sanya wa hannu a ranar 17 ga Oktoba, 2026, ƙungiyar ta bayyana cewa matakin dakatar da yajin aikin ya biyo bayan ganawar da ta yi da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a ranar 16 ga Oktoba, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa ganawar ta bai wa ƙungiyar damar tattauna ƙorafe-ƙorafenta da gwamnatin jihar, inda aka samu wasu alƙawura da suka shafi inganta jin daɗin ma’aikatan lafiya da warware matsalolin da suka dade suna fuskanta.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, daga cikin alƙawuran da gwamnatin ta bayar akwai sake buɗe tattaunawa kan tsarin albashi da alawus-alawus na CONHESS, da nufin duba yadda za a magance matsalolin da suka shafi tsarin biyan ma’aikatan lafiya.

Haka kuma, gwamnatin ta yi alƙawarin biyan wasu alawus-alawus da ake bin ma’aikatan, tare da warware matsalar tsallake matakin CONHESS 10 ga jami’an lafiya da suka cika sharuddan cancantar hawa wannan matsayi.

Bayan samun waɗannan alƙawura, ƙungiyar ta umarci dukkan mambobinta da su koma bakin aikinsu daga ƙarfe 12 na daren ranar 18 ga Oktoba, 2026, domin ci gaba da gudanar da ayyukan jinya da sauran ayyukan gudanarwa a cibiyoyin lafiya da ke faɗin jihar.

Ƙungiyar ta kuma nuna godiyarta ga mambobinta bisa haƙuri, jajircewa da haɗin kan da suka nuna a lokacin yajin aikin, tare da yabawa Gwamna Dikko Umaru Radda bisa sa hannun da ya yi wajen shiga tsakani da neman mafita ga matsalolin.

Dakatar da yajin aikin na zuwa ne a matsayin wani mataki na bai wa gwamnatin jihar damar cika alƙawuran da ta ɗauka, yayin da ake sa ran ci gaba da tattaunawa domin samun mafita mai ɗorewa ga ƙorafe-ƙorafen ma’aikatan lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments