Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiDubban Magoya Bayan APC Sun Tarbi Radda a Malumfashi

Dubban Magoya Bayan APC Sun Tarbi Radda a Malumfashi

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana karamar hukumar Malumfashi a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyin siyasa a jihar, bayan dubban magoya bayan APC sun yi dandazo domin tarbarsa a garin.

Radda ya bayyana hakan ne yayin gangamin neman goyon bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tasa a zaben 2027, wanda ya gudana a filin wasa na Malumfashi.

Gwamnan ya ce yadda jama’a suka fito kwansu da kwarkwatarsu, tare da nuna farin ciki da goyon baya, ya tabbatar da muhimmancin Malumfashi a siyasar jihar.

Ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana wasu nasarorin gwamnatinsa, yana mai cewa irin ayyukan da aka gudanar su ne dalilan da ya kamata al’umma su sake ba APC dama a zaben 2027.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben, Dakta Mustapha Inuwa, ya bukaci al’ummar Malumfashi da su mara wa APC baya, yana mai cewa jam’iyyar ce ke da tsari da kyakkyawar manufa wajen yi wa al’umma hidima.

Inuwa ya kuma bayyana cewa rashin adalcin da suka ce sun fuskanta a ADC ne ya sa suka fice daga jam’iyyar zuwa APC.

Shi ma Sanata Hadi Sirika ya bayyana taruwar dubban magoya bayan APC a wajen gangamin a matsayin wata alama da ke nuna karfin jam’iyyar da shirinta na tunkarar zaben 2027.

Gangamin ya samu halartar Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Jobe; Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zabe, Arc. Ahmed Musa Dangiwa; Shugaban APC na jihar, Dakta Bishir Gambo Saulawa; da Alhaji Mustapha Inuwa.

Sauran sun hada da Sakataren tawagar yakin neman zaben, Alhaji Abdullahi Turaji; Sanata Muntari Dandutse; dan majalisar wakilai mai wakiltar Malumfashi/Kafur, Hon. Ibrahim Kafur, da sauran mambobin tawagar.

Taron ya kasance wani bangare na gangamin da tawagar yakin neman zaben Tinubu/Dikko ke gudanarwa domin karfafa goyon bayan jam’iyyar APC gabanin babban zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments