Wani dattijo mai shekaru 107, mai suna Malam Abubakar Sadik, wanda aka fi sani da Baba Sadi, ya rasu bayan maciji ya sare shi a gidansa da ke yankin Bayan Dogon Bene, cikin Ƙaramar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Rahotanni sun bayyana cewa, rasuwar dattijon ta zo ne kwanaki biyu bayan shi da wani jikansa sun kashe maciji a kan katangar gidansu.
An ce wani macijin ne ya sake shiga ɗakinsa inda ya sare shi a lokacin da yake kwance, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Haka kuma, kwanaki biyu bayan rasuwar dattijon, maciji ya sare jikansa mai suna Abubakar Abdullahi, amma ya tsira bayan an yi ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
