Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da jami’an tsaron da za su rinka kula da dazuzzuka, waɗanda aka dauki jami’ai 1,008 domin ƙarfafa matakan tsaro da kuma dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a sassan jihar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da jami’an ne a ranar Juma’a, tare da bikin yaye su da aka gudanar a filin taro na People’s Square da ke gidan gwamnatin jihar Katsina.
Tunda farko, Radda ya bukaci jami’an da su kasance masu kishin ƙasa, jajircewa da ƙwarewa wajen gudanar da aikinsu, tare da tabbatar da kare dazuzzukan jihar daga ayyukan ’yan bindiga, ’yan ta’adda, masu satar shanu da kuma masu sare itatuwa ba bisa ka’ida ba.
Gwamnan ya ce jami’an za su yi aiki tare da mambobin rundunar tsaron al’umma ta Community Watch Corps (CWC) guda kusan 3,000 da gwamnatin jihar ta kafa, da kuma sauran jami’an tsaro, ’yan sintiri da mafarauta domin tabbatar da tsaron yankunan dazuzzuka.
Ya kuma tabbatar wa jami’an cewa gwamnatinsa za ta samar musu da kayan aikin da suke bukata domin saukaka musu gudanar da ayyukansu na kare dazuzzuka da al’ummomin da ke makwabtaka da su.
Haka kuma, Radda ya bayyana cewa, a baya dazuzzukan jihar sun kasance wuraren da al’ummomin da ke kewaye da su ke samun abin dogaro da kai, amma daga bisani sun koma maboyar ’yan bindiga da sauran miyagun mutane.
Sai dai ya ce matakan da gwamnatinsa ta dauka, musamman kafa rundunar Community Watch Corps da tallafa wa hukumomin tsaro na kasa, sun taimaka matuka wajen rage ayyukan ’yan bindiga da ta’addanci a jihar da kuma dazuzzukanta.
Kazalika, Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesansa na kafa rundunar jami’an tsaron dazuzzuka a jihohin ƙasar, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tabbatar da tsaron dazuzzukan Najeriya.
Shi ma da yake jawabi a wajen bikin, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ce za a tura jami’an 1,008 nan take zuwa yankunan da ke fama da matsalolin tsaro domin tattara bayanan sirri da kare dazuzzuka da kuma taimakawa wajen dakile ayyukan miyagu.
Ribadu, wanda tsohon mataimakin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), I.O. Shotayo, ya wakilta, ya bukaci jami’an da su kasance masu ladabi, kwarewa da kuma mutunta haƙƙin bil’adama yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce ana da kyakkyawan fata cewa jami’an za su yi aiki cikin jarumtaka, gaskiya da amana domin dawo da cikakken tsaro a dukkan dazuzzukan ƙasar.
A nasa jawabin, kwamandan da ya jagoranci horas da jami’an, Laftanar Kanal George Agar, ya bayyana cewa jami’an 1,008 sun kunshi maza 990 da mata 18, wadanda suka shafe tsawon makonni takwas suna samun horo kan dabarun yaƙi da kuma amfani da bindigogi kirar AK-47.
Ya ce an horas da su kan dabarun tunkarar ’yan ta’adda, ceto mutanen da aka sace, tattara bayanan sirri, gudanar da ayyuka cikin duhu da kuma dakile sare itatuwa ba bisa ka’ida ba.
Rahoton ya ce galibin jami’an an zabo su ne daga al’ummomin da ke kusa da dazuzzukan da matsalar rashin tsaro ta fi shafa, inda ake sa ran za su fara gudanar da ayyukansu nan take.
