Wani mazaunin Kwanar Dangora a Jihar Kano, Muhammad Bello, ya ce ya rasa dukiyarsa da hanyoyin samun abin dogaro da kai bayan shafe shekaru 11 a gidan yari ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Bello ya ce an kama shi ne a shekarar 2015 bisa zargin hannu a kisan kai, amma daga baya wanda ake zargi da kai ƙarar, Umar Gano, ya musanta cewa ya tuhume shi da laifin.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, An sako shi ne a ranar 14 ga Agustan 2026, bisa umarnin Babbar Alƙalin Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Aboki.
Ya bayyana cewa kafin kama shi, noma da kiwon dabbobi ne hanyoyin da yake samun abin rayuwa, amma zaman gidan yarin ya lalata masa sana’o’i, lamarin da ya sa yake ƙoƙarin sake gina rayuwarsa.
A nasa ɓangaren, lauyansa, Usman Fari, ya ce zai shigar da ƙarar neman diyyar Naira miliyan 900 a kan rundunar ’yan sanda da Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano bisa zargin tsare Bello ba bisa ƙa’ida ba.
