Wednesday, November 18, 2026
HomeLabaraiTinubu Ya Amince da Samar da Tashar Tsandauri a Jihar Kebbi

Tinubu Ya Amince da Samar da Tashar Tsandauri a Jihar Kebbi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar samar da tashar tsandauri (Inland Dry Port) a Jihar Kebbi, yana mai cewa an amince da aikin domin biyan buƙatar jihar na inganta harkokin kasuwanci da sufuri.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Jihar Kebbi domin neman goyon bayan al’umma a yunƙurinsa na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

A yayin jawabin nasa, Shugaban Ƙasar ya ce ya karɓi buƙatun da Gwamnan Jihar Kebbi ya gabatar masa, ciki har da samar da tashar tsandauri, tare da wasu ayyukan hanyoyi da gyaran hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata.

“Na fahimci buƙatarku game da tashar tsandauri. An amince da ita. Kebbi tana buƙatar wannan aiki, kuma an amince da shi,” in ji Shugaban Ƙasar.

Tinubu ya kuma gode wa al’ummar Kebbi bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen 2023, inda ya bayyana cewa ya je jihar ne domin nuna godiya da kuma neman goyon bayansu a karo na biyu domin kammala ayyukan da ya fara.

Ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da aiki domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da samar da abubuwan more rayuwa.

Haka kuma, ya buƙaci matasa da sauran al’ummar jihar da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, tare da yin amfani da katin zaɓensu wajen shiga harkokin dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments