Dakarun rundunar Operation Enduring Peace sun kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifuka tare da kwato wayoyin hannu guda 38 da wasu kayayyakin da ake zargin sata ne a Jihar Filato.
Dakarun sun gudanar da samamen ne a sassa daban-daban na Karamar Hukumar Jos North, ciki har da Jos da Naraguta, inda suka kuma kwato babur da ake zargin sata ne, bindigar wasa da motar Mercedes-Benz E350.
Jami’in hulda da manema labarai na Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, ya ce kamen farko ya biyo bayan korafin fashi da makami da satar wayoyi da aka kai wa dakarun ranar 6 ga Nuwamba, 2026.
Ya bayyana cewa bayan samun rahoton, dakarun sun kai samame a otal din Prime House da ke kan titin Ring Road a Jos, inda suka kama mutum biyar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, wadanda aka kama sun hada da Tahir Suleiman mai shekaru 25, Muhammed Ahmed mai shekaru 25, Muhammed Labaran Haruna mai shekaru 27, Yahya Yunusa mai shekaru 20 da Aisha Mohammad mai shekaru 22.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da wayoyin hannu 38, jakunkunan waya 27, na’urorin MP3 guda uku, earpods guda biyu, kwamfutar HP, agogon zamani guda hudu, adda, na’urorin cajin waya guda hudu da motar Mercedes-Benz E350 mai lambar rajista Plateau BBK-01NB.
A wani samamen daban, dakarun da ke Naraguta tare da hadin gwiwar jami’an kungiyar sa-kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) sun kama wasu mutane biyu, Mudasiru Ishaq mai shekaru 27 da Hasiya Sani mai shekaru 22.
An ce an kama mutanen ne yayin sintiri, inda aka same su da babur kirar Boxer da ake zargin sata ne da kuma bindigar wasa.
Kyaftin Oteh ya ce za a mika dukkan wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato ga rundunar ’yan sandan Jihar Filato domin gudanar da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a gaban kotu.
