Ɗantakarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya yi alƙawarin cire ma’aikatan jihar daga tsarin fansho na PENCOM, tare da tabbatar da cewa ilimi da kiwon lafiya za su kasance kyauta idan ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Sanata Yakubu Lado ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓensa a cikin birnin Katsina, inda ya yi alƙawarin sauya tsarin kula da fanshon ma’aikatan gwamnati domin su riƙa samun abin da ya kamata bayan kammala aikinsu.
Ya ce idan aka zaɓe shi, zai cire ma’aikatan jihar daga tsarin fansho na haɗin gwiwa da gwamnatin jihar mai ci ta saka su, domin samar musu da tsarin da zai ba su damar samun isassun kuɗaɗen fansho bayan sun yi ritaya.
Haka kuma, ɗantakarar ya yi alƙawarin samar da kiwon lafiya kyauta ga dukkan al’ummar jihar, yana mai cewa babu wani ɗan ƙasa da ya kamata ya rasa ransa saboda rashin kuɗin sayen magani ko biyan kuɗin asibiti.
Ya ce idan saboda katin Naira 200 ko maganin Naira 1,000 ne kawai, marar lafiya zai iya rasa ransa, ya jaddada cewa idan Allah ya kai su ga nasara, zai tabbatar da cewa ana kula da mutane kyauta a asibitocin jihar.
Lado ya kuma bayyana aniyarsa ta gina manyan asibitoci guda uku a shiyyoyin siyasa uku na jihar Katsina, domin rage buƙatar al’ummar jihar ta fita zuwa wasu jihohi ko ƙasashen waje neman ingantacciyar kulawar lafiya.
A ɓangaren ilimi kuwa, Sanata Lado ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce harkar ilimi ta lalace a jihar, duk da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa jihar.
Ya ce duk da cewa jihar Katsina ta samu kuɗaɗen da ya kai naira tiriliyan uku daga gwamnatin tarayya, har yanzu akwai manyan ƙalubale a fannin ilimi da ke buƙatar kulawa ta musamman.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar mata, tare da samar da shirye-shiryen koyar da sana’o’i domin bai wa matasa da sauran al’umma damar dogaro da kansu ta hanyar sana’o’in hannu.
Kazalika, Dangane da matsalar tsaro kuwa, ɗan takarar ya jaddada cewa zai ɗauki matakan magance matsalar cikin ƙanƙanin lokaci idan aka zaɓe shi, yana mai cewa zai yi ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a sassa daban-daban na jihar.
Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana waɗannan alƙawura ne a matsayin wasu daga cikin manufofin da yake son aiwatarwa idan ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Katsina.
