Monday, November 23, 2026
HomeLabaraiAn Gano Gawar Jariri a Kano, Kasa da Sa’o’i 24 Bayan Samun...

An Gano Gawar Jariri a Kano, Kasa da Sa’o’i 24 Bayan Samun Tagwaye a Dorayi

An gano gawar wani jariri a unguwar Kofar Na’isa da ke birnin Kano, ƙasa da sa’o’i 24 bayan gano wasu jarirai tagwaye biyu a unguwar Dorayi.

Wani ɗan gwagwarmaya, Comrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an gano gawar jaririn da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau.

A cewarsa, wani yaro ne ya buɗe wata leda da aka ajiye a wurin, inda ya tarar da gawar jaririn a cikinta.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya ƙara tayar da hankalin al’ummar Kano, musamman bisa yawaitar rahotannin gano jarirai da aka yi watsi da su a sassa daban-daban na birnin.

Hakan ya sake janyo kira ga hukumomin tsaro da na jin daɗin jama’a da su gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan dakile irin waɗannan al’amura.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments