An kashe akalla Fulani 64 a hare-haren ramuwar gayya da aka kai a wasu al’ummomi biyu na Wawa da Gada Oli, a jihar Neja, biyo bayan kisan wani basarake da wasu mazauna ƙauyen Lumma Ba’are.
Rahoton jaridar Peoples Gazette ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Lumma Ba’are ranar Asabar, inda suka kashe tare da ƙona shugaban ƙauyen, Bawa Muhammad, da wasu mazauna yankin.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jihar Neja, Ardo Umar Lapai, ya ce an kashe Fulani sama da 64 a hare-haren ramuwar gayya da aka kai tsakanin ranar Asabar da Lahadi, kuma tuni aka binne gawarwakin.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta gaggauta tura jami’an tsaro yankunan domin kare rayukan al’umma da kuma kamo waɗanda suka aikata kisan.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar harin farko, inda ya ce mutane biyar ne aka kashe a ƙauyen Lumma Ba’are.
Ya kuma bayyana cewa an tura haɗin gwiwar jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.
