Thursday, November 26, 2026
HomeLabarai'Yan Takarar Sanata 8 Sun Janye Wa Abdulaziz Yari

‘Yan Takarar Sanata 8 Sun Janye Wa Abdulaziz Yari

Ƴan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Yamma guda takwas daga jam’iyyun siyasa daban-daban sun janye takararsu tare da bayyana goyon bayansu ga Sanata mai ci, Abdulaziz Yari na jam’iyyar APC, gabanin zaɓen 2027.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai kula da ofishin mazabar Yari, Sha’ayau’u Sarkinfawa, ya fitar ranar Laraba a Gusau.

’Yan takarar sun sanar da matsayar tasu ne yayin ziyarar da suka kai ofishin Yari da ke Talata Mafara.

Wadanda suka janye takarar sun haɗa da Sani Abdullahi na APP, Ibrahim Anka na NDP, Sanusi Mohammed na YPP, Yahaya Aliyu na LP, Abdulmalik Adamu na APM, Murtala Abubakar na Accord, Anas Usman na SDP da Aishat S-Pawa ta ADP.

Da yake magana a madadinsu, Sani Abdullahi ya ce sun ɗauki matakin ne domin amfanin al’ummar yankin, tare da alƙawarin mara wa Yari da Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar APC baya a zaɓen 2027.

Ya bayyana naɗin Yari a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a matsayin babban matsayi da ya kamata al’ummar Zamfara su mara masa baya.

A nasa martanin, Yari, wanda Sarkinfawa ya wakilta, ya gode wa ’yan takarar bisa matakin da suka ɗauka, tare da tabbatar musu da cewa za a ba su dama da karramawa a cikin jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa za a shigar da su cikin kwamitocin yaƙin neman zaɓen APC na mazabar sanatan, domin su taka rawa a sauran harkokin siyasa na yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments