Thursday, November 26, 2026
HomeLabaraiMutane Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata a Hanyar Zuwa Taron Tinubu...

Mutane Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata a Hanyar Zuwa Taron Tinubu a Borno

Mutane biyu sun rasu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyarsu ta zuwa halartar taron yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Maiduguri, Jihar Borno.

Arewa Updates ta rawaito cewa hakan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Gwamnan Jihar Borno Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dauda Iliya, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Biu zuwa Damaturu. Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Biu da iyalan waɗanda suka rasu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi da cikakkiyar lafiya.

Haka kuma, gwamnan ya jajanta wa al’ummar Damboa kan wani lamari da ya faru a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, duk da cewa sanarwar ba ta bayyana adadin waɗanda lamarin ya shafa ba.

Biyo bayan waɗannan al’amura, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin ɗage taron yaƙin neman zaɓen APC na yankin Kudancin Borno, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, zuwa ranar Laraba, 2 ga Disamba, 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments