Thursday, November 26, 2026
HomeLabaraiFursunoni 3 Sun Mutu Yayin Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yari a Kwara

Fursunoni 3 Sun Mutu Yayin Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yari a Kwara

Hukumar kula da gidajen Yari ta Najeriya (NCoS) ta ce fursunoni uku sun mutu yayin yunkurin tserewa daga gidan yarin Oketura da ke tsohon birnin Ilorin, jihar Kwara.

Babban Kwanturolan hukumar, Sylvester Nwakuche, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai Ilorin ranar Laraba.

Ya ce fursunoni bakwai ne suka yi yunkurin tserewa a ranar 18 ga Nuwamba, inda jami’an gidan yarin suka dakile biyar, yayin da biyu suka yi nasarar tserewa.

Ya bayyana cewa fursunoni uku daga cikin biyar da jami’an suka hana tserewa sun mutu a yayin lamarin.

Nwakuche ya ce ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai cewa duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci bisa doka.

Ya kuma bayyana cewa gidan yarin na Oketura tsohon gini ne da aka gina tun zamanin mulkin mallaka, kuma a halin yanzu yana fama da cunkoso.

Haka kuma, ya ce akwai fursunoni sama da 4,000 da aka yanke wa hukuncin kisa a gidajen yarin Najeriya, inda ya bukaci gwamnonin jihohi su sauya hukuncin zuwa daurin rai da rai idan ba za su sanya hannu kan takardun aiwatar da hukuncin kisan ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments