Thursday, November 26, 2026
HomeLabaraiTsagin Nafiu Bala a ADC Zai Fara Kamfen Din Neman Shugaban Kasa...

Tsagin Nafiu Bala a ADC Zai Fara Kamfen Din Neman Shugaban Kasa Mako Mai Zuwa

Tsagin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa mai wakiltar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala, ya ce zai fara kamfen ɗin neman shugabancin Najeriya a mako mai zuwa.

Bala ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya ce yana da yakinin cewa ’yan Najeriya na goyon bayansa da tafiyar siyasarsa, don haka ba ya tsammanin za a kai masa hari yayin kamfen ɗin.

Ya kuma bayyana cewa yana duba yiwuwar bai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, muƙamin Darakta-Janar na kwamitin kamfen ɗin, idan har Atiku ya koma jam’iyyar ADC yadda ya kamata.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin shugabanci a ADC tsakanin ɓangaren Bala da na tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

A ranar 5 ga Nuwamba, 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Mark, tare da rushe matakan da kwamitin ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Kotun ta kuma bayyana cewa takardar murabus ɗin da ake zargin Bala ya sanya wa hannu ba ta isa ta tabbatar da cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments