Thursday, November 26, 2026
HomeLabaraiAmnesty International Ta Bukaci A Binciki Barazanar Kisa Da ake Yi wa...

Amnesty International Ta Bukaci A Binciki Barazanar Kisa Da ake Yi wa Abdul Turaki

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta nuna damuwa kan barazanar kisa, cin zarafi da kuma gargadin amfani da karfin gwamnati wajen hallaka Abdul Turaki, wani mai tasiri a kafafen sada zumunta.

Amnesty ta ce barazanar da ake yi wa Turaki ta biyo bayan mako guda da ya fallasa wasu zarge-zargen mu’amalar siyasa da ake dangantawa da cin moriyar jama’a, a gaban babban zaben da ke tafe.

A cikin wani bidiyo da ya fitar a ranar 25 ga Nuwamba, 2026, Abdul Turaki ya yi zargin cewa rayuwarsa na cikin hadari tun bayan fallasa wasu mu’amalolin siyasa da ake ta magana a kansu, wadanda ya danganta da jam’iyyar APC mai mulki.

Kungiyar Amnesty International ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan zarge-zargen da Turaki ya yi, tare da daukar lamarin da muhimmanci da kuma tabbatar da cewa an kare rayuwarsa.

Ta ce wasu daga cikin masu yi masa barazanar sun nuna cewa za su iya gano inda yake, su aikata duk abin da suka ga dama ba tare da wani hukunci ya same su ba, lamarin da kungiyar ta ce yana bukatar daukar matakin gaggawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments