Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce mutane 74 sun mutu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin masu gadin al’ummar Kambari da makiyayan Fulani a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai fadar Sarkin Borgu, Alhaji Halilu Sani Dantoro, a garin New Bussa.
Rikicin ya biyo bayan harin da wasu ’yan bindiga suka kai ƙauyen Lumman-Ba’are, inda suka kashe dagacin garin, Mallam Bawa Muhammad, matarsa da ’ya’yansa uku, tare da ƙona fadarsa.
Bayan harin ne aka samu zargin kai hare-haren ramuwar gayya, lamarin da ya janyo asarar rayuka da lalata wasu al’ummomi.
Gwamna Bago ya buƙaci ɓangarorin biyu su ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya, yana mai sanar da bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga kowace iyali da ta rasa ɗan uwanta a rikicin.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta gudanar da bincike kan barnar da aka yi tare da sake gina al’ummomin da aka ƙona.
A wani mataki na ƙarfafa tsaro, Sufeto Janar na ’yansanda, Olatunji Rilwan-Disu, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an rundunar yaƙi da ta’addanci zuwa yankin.
Mataimakin Sufeto Janar na ’yansanda, Shehu Umar Nadada, ya kuma gargaɗi al’umma da kada su bari ayyukan ’yan bindiga su rikide zuwa rikicin ƙabilanci.
