Saturday, November 28, 2026
HomeLabaraiJami’ar Northwest Ta Za Ta Fara Hukunta Daliban da Ke Baiwa Malamai...

Jami’ar Northwest Ta Za Ta Fara Hukunta Daliban da Ke Baiwa Malamai Kyaututtuka

Jami’ar Northwest da ke Kano ta haramta wa ɗalibai da malamai musayar kyaututtuka, tana mai bayyana hakan a matsayin cin hanci da rashawa da kuma ɓata sunan jami’ar.

Mahukuntan jami’ar sun ce ta ɗauki matakin ne bayan lura da yadda ɗalibai ke ba wa malaman da suka yi fice a fannoni daban-daban kyaututtuka, musamman waɗanda aka zaɓa a matsayin mafi ƙwazon malamai ko masu kula da matakai.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Magatakardar jami’ar, Isyaku Adamu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce jami’ar ta sanya dokar hana bayarwa ko karɓar kowace irin kyauta tsakanin ɗalibai da ma’aikata, ba tare da la’akari da kyakkyawar manufar da ke tattare da hakan ba.

A cewarsa, wannan dabi’a na cikin manyan laifuffukan da dokokin jami’ar suka haramta, kamar yadda kundin ƙa’idojin aiki da gudanarwa na shekarar 2025 ya tanada.

Sanarwar ta ce duk ma’aikaci ko ɗalibin da aka samu yana bayarwa ko karɓar kyauta dangane da ayyukan jami’ar zai fuskanci matakin ladabtarwa.

Adamu ya buƙaci ɗalibai da ma’aikatan jami’ar su kiyaye dokoki da ƙa’idojin aiki da ɗabi’a domin kauce wa hukunci.

Jami’ar Northwest ta Kano jami’a ce mallakin gwamnatin jihar, wadda aka kafa a shekarar 2012. An sauya mata suna zuwa Yusuf Maitama Sule University a shekarar 2017, kafin daga bisani ta koma tsohon sunanta a shekarar 2024.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments