Saturday, November 28, 2026
HomeLabaraiBa Zan Yi Atiku ba Ko da Kuwa Peter Obi Ya Janye...

Ba Zan Yi Atiku ba Ko da Kuwa Peter Obi Ya Janye Masa– Buba Galadima

Ba Jigo a jam’iyyar NDC, Alhaji Buba Galadima, ya ce ba zai goyi bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ba idan Peter Obi ya janye masa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Galadima ya bayyana cewa Obi ne mutumin da ya fi dacewa sauran ‘yan takarar hamayya su mara wa baya, yana mai cewa tikitin Obi da Rabiu Kwankwaso zai iya haɗa kan ‘yan Najeriya.

A wata hira da tashar ARISE NEWS, Galadima ya bayyana tikitin a matsayin wanda zai kawo sulhu da haɗin kan ƙasa.

Ya ce goyon bayansa ga Obi ya samo asali ne daga buƙatar bai wa yankin Kudu maso Gabas damar samar da shugaban ƙasa, domin samun damar jin cewa suna cikin tafiyar ƙasa.

“Ba zan goyi bayan Atiku ba, domin tikitin zai faɗi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar matashi mai kuzari wanda zai iya gudanar da ayyukan ƙasa da kansa, ba tare da dogaro da wasu wajen gudanar da mulki ba.

Haka kuma, Galadima ya nuna shakku kan yiwuwar haɗin kan jam’iyyun adawa ya yi nasara, tare da zargin APC da yunƙurin tsoratar da ‘yan adawa da hana su gudanar da harkokin kamfen cikin ’yanci.

Ya buƙaci Majalisar Ƙasa (National Council of State), tsohon shugaban ƙasa Abdulsalami Abubakar da kwamitin zaman lafiya na ƙasa su shiga tsakani domin tabbatar da zaman lafiya da kare dimokuraɗiyya gabanin zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments