A wani muhimmin mataki na gyaran hali da rayuwar ɗaurarru, fursunoni 58 a jihar Kano ne su ka zana jarabawar kammala makarantar sakandire ta kasa, NECO ta 2025.
Hukumar Kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, reshen jihar Kano ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa a yau Litinin, inda ta bayyana wannan ci gaba a matsayin babban nasara wajen kokarin gyara da mayar da fursunoni cikin al’umma.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan K/Nasarawa, ya sanya wa hannu, wannan nasara ta samu ne sakamakon goyon bayan gwamnatin jihar Kano wadda ta biya kuɗin rajistar dukkan fursunonin da suke zana jarabawar.
“Goyon bayan da mai girma Gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayar ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da jin daɗi, gyaran hali da kuma sake shigar da fursunoni cikin al’umma,” inji sanarwar.
Hukumar ta bayyana godiyarta ga Gwamna Yusuf saboda “goyon bayan sa mara yankewa da haɗin kai,” tana mai cewa wannan taimako zai karfafa gwiwar fursunonin tare da ba su wata dama ta biyu wajen samun ilimi da kyakkyawar makoma.
“Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, reshen jihar Kano, za ta ci gaba da tabbatar da yanayi mai kyau na gyaran hali da tarbiyya ga fursunoni, kuma muna alfahari da samun goyon bayan gwamnatin jihar Kano wajen wannan kokari,” inji sanarwa.