Riƙaƙƙen ɗan bindiga da aka daɗe ana nema, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su, tare da amincewa da dakatar da hare-haren da ke hana manoma shiga gonaki a ƙaramar hukumar Shinkafi, ta jihar Zamfara.
Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar sulhu da wasu malamai suka jagoranta, kamar yadda fitaccen malamin addini, Sheikh Musa Yusuf (Asadus-Sunnah), ya bayyana a wata Huɗuba da ya gabatar a Kaduna.
A cewarsa, tattaunawar ta samu ne da haɗin gwiwar al’ummar Shinkafi domin samun damar komawa gonaki cikin dajin Fakai. Taron sulhun ya gudana sau uku a watan Yuli, inda suka gana da manyan kwamandoji kamar Bello Turji, Dan Bakkolo (wanda ya ƙaryata jita-jitar mutuwarsa), Black, Kanawa da Malam Ila.
Ƴan bindigar sun miƙa wasu makamai, tare da amincewa da barin manoma su ci gaba da ayyukansu. A matsayin kyautar sulhu, Turji ya saki mutane 32 – ciki har da mata da yara, wasu daga cikinsu sun kwashe watanni a tsare, wasu kuma sun haihu a daji. Daya daga cikin su ya kamu da ciwon cizon maciji.
An kuma cimma matsaya cewa Fulani su riƙa yawo cikin yanci ba tare da fargabar farmakin sa-kai ba. Sheikh Yusuf ya ce zaman lafiya ya fara dawowa a Shinkafi sakamakon yarjejeniyar.