Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce rikicin Boko Haram ya fi rikice-rikicen da Najeriya ta taɓa fuskanta rikitarwa, yana mai bayyana cewa a wani lokaci mayakan ƙungiyar sun mallaki makamai fiye da sojojin ƙasa.
Jonathan ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafin tsohon babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) mai suna “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” a turance.
Ya ce rikicin Boko Haram ya sha bamban da na ‘yan tawayen Niger Delta saboda alaƙarsa da ƙasashen waje da akidar tsattsauran ra’ayi da kuma makaman zamani.
Tsohon shugaban ƙasar ya tuna cewa sace ɗaliban Chibok a 2014 ya kasance ɗaya daga cikin manyan raunuka da ba za a taɓa mantawa da su ba.
Jonathan ya jaddada cewa ba za a iya ɗaukar Boko Haram kawai a matsayin matsalar tsaro ba, yana mai kiran a haɗa ayyukan tsaro da kyakkyawar gwamnati, rage talauci, ƙarfafa matasa da tabbatar da adalci domin samun zaman lafiya na dindindin.
Taron ya samu halartar tsofaffin shugabanni da manyan jami’an tsaro, ministoci, da sarakunan gargajiya.