Hukumar Kwana-Kwana ta Nijar Kano ta tabbatar da rasuwar wata mata mai shekaru 96 sakamakon fadawa cikin ramin masai.
A wata sanarwa da kakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar a yau Juma’a, lamarin ya faru ne a kauyen Sarai da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
Ya ce hukumar ta karbi kiran gaggawa daga wani Usman Adamu a juya Alhamis cewa an gano gawar matar a cikin ramin masai, inda tuni jami’an hukumar su ka garzaya zuwa wajen da lamarin ya faru.
Ya ce jami’an suna zuwa su ka tarar da gawar matar mai suna Habiba Ado kwance cikin ruwan bahaya, inda ya kara da cewa tuni ma’aikatan su ka fito da ita kuma aka tabbatar da ta rasu.
Abdullahi ya kara da cewa dangin marigayiyar sun tabbatar wa da hukumar cewa tana da larurar ƙwaƙwalwa kuma an kwashi kwanaki hudu ana neman ta ba tare da sanin ta fada ramin ba sai a jiya Alhamis.
