HomeSashen HausaNajeriya Za Ta Ɗauki Sabbin Sojoji Dubu 24, Domin Inganta Tsoron Ƙasar

Najeriya Za Ta Ɗauki Sabbin Sojoji Dubu 24, Domin Inganta Tsoron Ƙasar

-

Babban Hafsan Sojojin Najeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana shirin daukar sabbin sojoji 24,000 domin kara karfin rundunar sojin kasar a yaki da matsalolin tsaro.

 

Janar Shaibu ya sanar da hakan ne a Kaduna yayin ziyarar aiki da ya kai Runduna ta 1, inda ya ce sabbin cibiyoyin horaswa guda uku—da Shugaba Bola Tinubu ya amince da su—za su samar da sojojin da suka kware a sabon dabarun yaki da horo na zamani.

 

Ya ce rundunar na fatan horas da sojoji 12,000 cikin watanni shida, kuma idan an gudanar da horaswa a matakai biyu za a iya samar da jimillar dakarun 24,000.

 

Babban hafsan ya jaddada cewa shirin ba wai kara yawan sojoji ba ne kawai, har ma da tabbatar da inganci, kwarewa, da shirin tunkarar barazanar tsaro da ke kara kamari a fadin kasar nan.

 

Ya kuma tabbatar da kudirin rundunar wajen inganta jin dadin ma’aikata a karkashin manufar “Soja Na Farko”.

 

Ana sa ran sabbin dakarun za su karfafa martanin sojoji, kare al’umma, da kuma inganta tsaro a manyan yankunan da ake fama da rikice-rikice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎DA ƊUMI-ƊUMI: ’Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 25 a Kebbi, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta

‎Fargaba da tashin hankali sun mamaye al’ummar Maga, cikin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, bayan wasu ’yan bindiga sun afka Government Girls Comprehensive Senior...

DA ƊUMI-ƊUMI: Soja AM Yerima Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yau A Abuja

Wani matashin jami’in Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Lt. A.M. Yarima, wanda ya yi rashin jituwa kwanan nan da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike,...

Most Popular