Ƙasar Mali, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Mulkin Soji, Kanal Assimi Goïta, ta ƙaddamar da wata sabuwar rundunar soji ta musamman mai suna Rapid Intervention Battalion (RIB).
Manufar kafa wannan runduna ita ce ƙarfafa ƙarfin aiki da ingancin rundunar Sojojin Mali (FAMa), tare da inganta saurin mayar da martani ga duk wani nau’in barazanar tsaro a fadin kasar.
Sabuwar rundunar za ta kasance mai saurin motsi da tsauraran horo, domin tinkarar hare-haren ‘yan ta’adda, rikice-rikicen cikin gida da kuma kare ikon ƙasa da lafiyar al’umma.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Mali ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan arewa da tsakiyar kasar, inda gwamnati ke ƙoƙarin ƙarfafa ikon ta da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
