HomeSashen HausaGamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya na shirin rajistar sabuwar jam'iyyar ADA don...

Gamayyar jam’iyyun adawa a Najeriya na shirin rajistar sabuwar jam’iyyar ADA don kifar da APC a zaɓen 2027

-

Jagororin jam’iyyun hamayya na Najeriya a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita domin fafatawa da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Nigerian Post ta samu cewa, tuni NNCG ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar INEC a hukumance, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar 20 ga Yunin.

A wasiƙar, sun rubuta cewa, “muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance ta zama jam’iyyar siyasa.”

Taken jam’iyyar dai shi ne ‘Adalci ga kowa’ sannan masara ce tambarinta.

Daga cikin na gaba-gaba wajen yunƙurin samar da haɗaka da za ta fuskanci jam’iyyar APC mai mulki akwai tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon shugaban majalisar dattawar ƙasar, Sanata David Mark da Umar Arɗo da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Hukumar NSCDC A Katsina Ta Yi Sabon Shugaba

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Katsina ta samu sabon kwamanda bayan sauyin shugabanci da ya gudana a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025.   A...

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Horas Da Malamai 250 Da Faransifal 50, Don Inganta Ilmin Jihar

Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko da na Sakandire a jihar Katsina, haɗin gwiwa da Majalisar Turai (British Council), ta ƙaddamar da wani muhimmin shirin horaswa...

Most Popular