HomeSashen HausaNDLEA sun shirya gangamin wayar da kan al'umma kan ta'ammali da miyagun...

NDLEA sun shirya gangamin wayar da kan al’umma kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Katsina

-

A ƙoƙarin daƙile fatauci da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Katsina haɗin guiwa da ƙungiyar Queen Dijah Women And Children Awareness Initiative, sun shirya gangamin ne domin faɗakar da al’umma kan illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi

Lokacin da suke gudanar da gangamin wayar da kan al’umma, sun zagaya a wasu titunan cikin garin Katsina, wanda ya yi dai-dai da ranar Laraba 25 ga watan Yuni a matsayin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don faɗakar da al’umma.

Taron ya samu mahalartar, al’umma daban-daban, da kuma jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC, da jami’an ƴan sanda, Sojoji da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defense, da kuma wasu ƙungiyoyin fararen hula masu yaƙi da shan miyagun kwayoyi a Katsina, daga ciki har da ƙungiyar dake rajin kare haƙƙin Mata da ƙananan Yara da masu buƙata ta musamman.

Nigerian Post ta samu cewa, mutane da dama ne suka goyi bayan Hukumar tare da yaba ma su a akan ƙwazon su na wayar da kai, gangamin bikin tunawa da ranar.

A jawabin kwamandan hukumar NDLEA a jihar Katsina, Sama’ila Ɗanmalam, ya ce sun shirya taron domin faɗakar da al’umma kan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi domin ganin cewa an samu al’umma tagari.

Ya ce, ita al’umma idan ta yi kyau kowanne ɓangare zai yi kyau kuma za a rinƙa samun kyakkyawan tattalin arzikin ƙasa, da kuma gujewa yawaitar samun mugayen laifuffuka a ƙasa.

Ya kuma gode ma jama’a da kuma gwamnatin jihar Katsina da ta ba su gudunmawa suka shirya taron, don wayar da kan jama’a kan illar sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, daga ciki har da jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

El-Rufa’i Ya Ce Tinubu Ba Zai Ci Zaɓe A 2027 Ba, Sai Ya Yi Da Ƙyar Zai Zo Na Uku

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba. Inda...

Sule Lamido Na Shirin Shiga Haɗaka Don Kawar Da Tinubu A 2027

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga kowace haɗakar jam'iyyun siyasa da nufin kawar da Shugaba Bola Tinubu...

Most Popular