HomeSashen HausaJirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa...

Jirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa Ta Zuwa Katsina

-

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin tsayar da wani jirgin sama na kamfanin Rano Air mai lamba 5N-BZY, biyo bayan wata matsala da aka ruwaito cewa injin jirgin ya tsaya cak yayin da yake kan hanyarsa daga Abuja zuwa Katsina.

Wannan shawarar ta biyo bayan tsauraran matakan da NCAA ke É—auka don tabbatar da bin Æ™a’idojin tsaron jiragen sama a duk kamfanonin jiragen sama da ke aiki a sararin samaniyar Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin tafiyar, an samu matsala a inji na farko na jirgin, wanda hakan ya sa aka ga hayaÆ™i a cikin jirgin. Nan take ma’aikatan jirgin suka kunna na’urar bada iskar oxygen tare da É—aukar duk matakan gaggawa don shirya sauka lafiya. Majiyoyi sun bayyana cewa hayaÆ™in ya É“ace kafin sauka, kuma jirgin ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba.

A wani rahoto da Katsina Post ta fitar, sai dai lamarin ya haifar da cikas ga jadawalin zirga-zirgar jiragen na Rano Air, inda ya bar fasinjojin da za su tashi daga Sokoto a filin jirgi. An tura wani jirgin ceto domin É—aukar fasinjojin Abuja-Katsina, amma an soke tafiyar ta Sokoto.

Rahoton farko daga NCAA ya nuna cewa, Sashen Kula da Ingancin Jiragen Sama ya bayar da umarnin tsayar da jirgin har sai an kammala cikakken bincike.

“Injiniyoyi suna binciken jirgin a halin yanzu don gano ainihin musabbabin matsalar injin da kuma hayaÆ™in,” in ji rahoton.

Hukumar ta NCAA ta sake jaddada cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba wajen bin ka’idojin jiragen sama, ko da kuwa hakan zai haifar da cikas ga ayyukan zirga-zirgar jiragen.

NCAA ta yi alkawarin fitar da Karin bayani kan lamarin da zarar an kammala bincike kan jirgin mai lamba 5N-BZY.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nasarori 12 Da Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya Kafa A Shugabancin APC

Jerin basarori 12 da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa da babu shugabanta da ya taɓa kafawa a cikin...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda yake jagorantar wata babbar tawaga domin halartar...

Most Popular