Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ce ba komai ne ya sa masu haɗaka suke kumfar baki ba shi ne, saboda rashin samun muƙami wanda har suka ƙirƙiro wai wata haɗaka da suke ganin kamar al’umma za su yarda da su.
Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin Sunrise Daily na Channels TV, ranar Talata, inda ya ke cewa, lokaci ya wuce da za a ci gaba da yaudarar ‘yan Najeriya domin kar suke kallon kowa.
A cewar sa, waɗanda suke ƙoƙarin yin haɗakar su ne sukai mulki jiya, kuma suna sane da tarihin kowa, kuma sun san duk abin da suka aikata mai kyau ko marar kyau a lokacin da suke cikin gwamnatin baya.
Haka kuma, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya caccaki haɗakar tare da ɗora ayar tambaya sahihancin manufarta da kuma gaskiyar dalilin kafuwarta, inda ya jaddada cewa, yanzu ya rage ma ‘yan Najeriya sai su yi alƙalanci da kan su.