HomeSashen HausaRikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai A Haɗakar Jam'iyyar ADC

Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai A Haɗakar Jam’iyyar ADC

-

Wasu mambobin jam’iyyar ADC guda uku sun shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda suke ƙalubalantar sahihancin naɗin sabbin shugabannin rikon kwarya da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ke jagoranta.

A cikin ƙarar da suka shigar ranar 4 ga watan Yuli 2025, masu ƙarar sun shigar da karar Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Tolu, da Haruna Ismaila, yayi da suka nemi kotu ta tantance halascin naɗin sabbin shugabannin jam’iyyar da suka ce an yi ba bisa ƙa’ida ba.

Kamar yadda Nigerian Post ta samu daga DCL Hausa, sun bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar, Nwosu, bai da hurumin kiran taron NWC ko NEC ko wani taron jam’iyyar kasancewar wa’adinsa ya ƙare.

Haka kuma, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, sun ce naɗin David Mark, Rauf Aregbesola, da Bolaji Abdullahi a matsayin shugabanni na rikon kwarya bai da madogara a doka, don haka suna neman kotu ta ayyana naɗin a matsayin maras inganci, inda suka roƙi kotu ta hana INEC amincewa da su a matsayin shugabannin jam’iyyar ADC na riƙon kwarya domin bin doka da oda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular